23 Janairu 2021 - 12:42
Zainab Sulaimani: Trump Ya Bar Mulki Kaskantacce Alhali Mahaifina Ya Bar Duniya Cikin Daukaka

Ɗiyar tsohon kwamandan rundunar Ƙudus ta dakarun kare juyin juya halin Musulunci na ƙasar Iran, Janar Ƙasim Sulaimani ta bayyana cewar mahaifinta ya bar duniya cikin ɗaukaka, alhali kuwa Donald Trump wanda ya ba da umurnin kashe shi ya bar mulkin Amurkan cikin ƙasƙanci da karayar zuci.

ABNA24 : Zainab Ƙasim Sulaimani ta bayyana hakan ne a wani saƙo da ta wallafa a shafinta na Twitter bayan rantsar da sabon shugaban Amurka Joe Biden da kuma kawo ƙarshen mulkin Trump ɗin inda ta ce: Ko shakka babu jinin Janar Sulaimani zai ci gaba da jin diddigin Trump wanda zai ci gaba da zama cikin tsoro da fargaba tsawon rayuwarsa.

Zainab Sulaimani ta ƙara da cewa: Mr. Trump ka kashe mahaifina, Janar ɗin da yayi nasara a kan ƙungiyoyin ISIS/Al-Qaeda, da burin cewa za ka zama wani gwarzo, to amma maimakon hakan sai ga shi ka sha kaye, ka zama ƙasƙantacce wanda kuma zai ci gaba da rayuwa cikin tsoro.

A ranar 3 ga watan Janairun 2020 ne dai tsohon shugaban Amurka Donald Trump ɗin ya ba da umurnin kashe Janar Qasim Sulaimani da Abu Mahdi al-Muhandis mataimakin kwamandan dakarun sa kai na ƙasar Iraƙi, Hashd al-Sha’abi a kusa da filin jirgin saman birnin Bagadaza, babban birnin ƙasar Iraƙin a lokacin da Janar Sulaimanin ya kai ziyara ƙasar Iraƙin.

Tun bayan lokacin dai jami’an ƙasar Iran sun sanar da cewa ba za su taba zuba ido haka kawai ba tare da ɗaukar fansar jinin Janar ɗin ba. A kwanakin baya ma dai Iran ta shigar da ƙara da kuma buƙatar ‘yan sandan ƙasa da ƙasa Interpol da su kamo mata Trump da wasu muƙarrabansa da suke da hannu cikin wannan ɗanyen aiki.

342/